Umar M Shareef

Mawaƙin hausa a najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Umar Muhammad Shareef Wanda aka fi sani da Umar M Shareef (An haife shi a shekara ta alif dari tara da tamanin da takwas miladiyya 8 April 1989) a cikin garin Kaduna. Fitaccen mawakin Hausa ne na soyayya haka nan kuma mai shirya fina finan Hausa kuma jarumi a masana'antar ta Kannywood.

Quick facts Rayuwa, Haihuwa ...
Thumb
JS_Icon_Edit

Umar M Shareef, fitaccen mawakin Hausa ne, na soyayya, sannan an san shi a matsayin jarumi a masana'antar Kanywood. Umar M Shareef yana da kyakkyawar alaka da dukkan yan wasan kwaikwayon Hausa na Kanywood musamman Ali Nuhu wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen fito da jarumin, sannan ya samu lambar yabo daga bangare daban-daban.

Remove ads

Tarihi.

An haifi jarumin a shekarar 1989 a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, shahararren mawakin Hausa ne sannan kuma jarumi ne a masana'antar kannywood wanda ya shahara a kasar Najeriya da sauran kasashen afrika. Jarumi kuma mawaki yana da mabiya a kasashe da dama a fadin duniya, Wanda a kullum burinsa bai wuce ya ga ya burgesu ba.[1]

Karatu.

Jarumin ya fara karatun Qur'ani tun yana yaro a gida kafin ya shiga makarantar boko wacce izuwa yanzu ya kai matakin digiri wanda ya ke yi a Jami'ar Jihar Kaduna (KASU)

Wakoki.

Asalin fara wakarsa ta dalilin wata yarinya da yake so amma ya kasa sanar mata har izuwa lokacin da ya yanke shawarar tinkararta amma sai bata fito ba hakan ya sa ya tafi yana rera waka. Jarumin ya jima yana waka amma taurarinsa ya fara haskawa ne a shekara ta 2007 sannan yayi wakoki da dama a bangare daban-daban na soyayya, siyasa, da wakokin biki da suka haɗa da;

  • Jinin jikina
  • Sareena
  • Jirginso
  • Ruwan dare
  • Hafiz
  • Ciwon idanuna
  • Arewa
  • Ciwon so
  • Mariya
  • Wazana ba kaina
  • Aisha
  • Mansoor
  • Tsintuwa

Albums/Kundi

Sannan yanzu yayi albums da dama kamar su:

Ƙarin bayanai Sunan Kundi/Album, Shekarar fita ...

|Lokaci Yayi || 2024 |} |Fari Jini Ep || 2023 Gidan sarauta

Haɗaka

Sannan yayi wakoki da mawaka da dama kamarsu;

  1. Nura M Inuwa
  2. Lilin Baba
  3. Abdul D one
  4. Hamisu Breaker
  5. Adam A Zango da sauransu.

Fina-finai

Ya fito a finafinai da dama kamarsu;

  • Mansoor
  • Sareena
  • Mujadala
  • Hafeez
  • Mariya
  • Tsakaninmu
  • Ciwon idanu na
  • Kar ki manta Da ni
  • Nass

Bugu da kari mafi yawan fina-finansa ya fito ne a companin FKD wanda mallakin Ali Nuhu ne. Sannan shi ne mamallakin Shareef studio wanda sun shirya fina-finai kamar su

  • Zarah
  • Jinin jikina

Karramawa

Jarumin ya sha karban kyautar karramawa da kyautar girmamawa da dama a fadin duniya daga kungiyoyi da dama kamar su

  1. Kannywood films award
  2. Afrikan actors

Da sauransu

Rayuwa ta sirri

Ya kasance daga cikin manyan jaruman da suka ziyarci sassa daban-daban na duniya. Jarumin ya ziyarci kasashe da dama wadda suka hada da : Niger, Ghana, Cameron, Chad, da sauransu.[ana buƙatar hujja]

Iyali

Umar M Shareef yana da mata daya Maryam da yara biyu jarumin da kuma Hafsat.

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads