Ali Nuhu
Dan wasan Kuma mai bada umarnin a Shirin wasan ƙwaiƙwayo, an haife shi a shekarata 1974 From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Ali Nuhu Mohammed An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan Maris na shekarar alif da dari tara da saba'in da hudu (1974) a garin Maiduguri dake Jihar Borno,. Ya girma a jihar Kano, mahaifinsa dan Balanga ne a jihar Gombe dake ((Arewacin Najeriya|arewacin Nigeriya)).


Ali Nuhu ya fito daga kabilar Tangale Waja, cikakken sunan mahaifinsa shine Nuhu Poloma wanda dan asalin jihar Gombe ne.
Ali Nuhu ya girma a hannun mahaifiyar sa a jihar Kano, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar alif da dari tara da casa'in da tara (1999) miladiyya . Shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekara ta dubu biyu da ashirin (2020). Ali Nuhu jarumine a harkar fina finai, sannan marubucine, mai bada umarni kuma furodusa ne a masana,antar shirya finafinai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma wasu lokutan yakan yi rawa a wasu fina-finai.
Ali Nuhu yana fina-finan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jaruman da suka kafa masana'antar shirya finafinai ta kannywood.
Shekarun sa 51 a shekarar 2025, ya kuma karanci geography a jami'ar Jos wato University of Jos a turance.
Mutane suna masa inkiya da "sarki Ali Nuhu" (King of kannywood), wanda a kalla zuwa yanzu ya fito a finafinai sama da dari biyar (500+) wanda ya samu lambobin yabo da dama. Ko a shekarar 2023 saida ya samu lambar yabon "Best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA 2023)".
Ali Nuhu ya fara harkar fim tun a shekarar alif da dari tara da casa'in da tara (1999) miladiyya wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken "ABIN SIRRI NE" ya kuma fito a finafinan masana'antar shirya finafinai ta kudanci najeriya NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.
Jarumin yana da mata daya da yara biyu (2) Ahmad da fatima.

A shekarar 2024 shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban masana'antar fina-finai ta Najeriya gaba daya.
Remove ads
Farkon rayuwa
An haifi Ali Nuhu Muhammad a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe dake a arewacin Najeriya da mahaifiyarsa mai suna Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.[1]
Aure
Ali Nuhu yana da mata daya da Yara guda biyu Ahmad Ali nuhu da Fatima Ali nuhu.
Ilimi
Ali ya yi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin na fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[2]
Sana'a
Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama dayan finafinan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummuwa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[3]
Shugaban Hukumar Fina-finai ta Najeriya
A shekarar 2024 shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar kula da fina-finai ta Najeriya.[4]
Remove ads
Mabiya
inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da mutane dubu dari da arba'in 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da mutane dubu uku 3,000,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da milyan mutane dubu dari 1,000,000.[5][6]
Fina finai a Kannywood
(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.
Remove ads
Bada umarni
2024
Remove ads
Lamban girma
Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana'antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina-finai.[7][8]
Remove ads
Hotuna

Ali Nuhu
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads