Gidauniyar Wikimedia
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Gidauniyar Wikimedia ('WMF, ko a takaice Wikimedia) wata Gidauniya ce a Amurka wanda bana samar da jari bace sai dai ma'aikatar taimako da ke da helkwata a birnin San Francisco, California.[1] Anfi sanin kamfanin da daukan nauyin shafukan Wikipidiya, wani mashahurin kundin ilimi na yanar gizo, har wayau ta na daukan nauyin wasu shafuka masu alaka da kuma Mediawiki, wata softwaya ta yanar gizo.[2][3][4][5]

Jimmy Wales ne ya kirkiri Gidauniyar ta Wikipedia a shekara ta 2003 a St. Petersburg, Florida, a matsayin hanyar tallafawa Wikipedia, Wikitionary da sauran manhajojinta wadanda a da Bomis ne ke daukan nauyinsu.[6][7] Gidauniyar ta na ciyar da kanta ta hanyar miliyoyin kudade da ake samo daga makaranta shafukan Wikipidiya, wadanda ake tattarawa ta hanyar kamfe na shekara-shekara da kuma neman tallafi don Wikipidiya. Akwai tallafe-tallafe na musamman daga kamfanonin fasaha da dama da kuma kungiyoyin jin kan jama'a.
Gidauniyar ta habaka cikin sauri tun lokacin da aka kafa ta. Yi zuwa shhekara ta 2021, ta dauki ma'aikata da masu ayyukan kwantiragi sama da mutum 550, tare da samun kudin shiga a duk shekara da suka kai kimanin dala miliyan US$160, kudaden kuwa da ake kashewa a duk shekara sun kai kimanin dala miliyan 110, kuma habakar tallafi na sama da dala miliyan 100 a bisa watan Junin 2021.
Remove ads
Kuduri
Gidauniyar Wikimedia Foundation nada Kuduri karfafawa da kuma shigar da mutane daga sassa daban-daban na duniya wajen tattarawa da kuma habaka bayanai na ilimi a karkashin lasisi ta kyauta ko kuma ajiya don amfanin al'umma, da kuma yada shi ilimin da kyau a sassa daban daban na duniya.[8]
Don tabbatar da wannan kuduri, Gidauniyar na samar da kayan aiki na fasaha da na kungiyoyi don tallafawa mambobin al'ummomi wajen habaka bayanai akan wiki a cikin harsuna daban daban.[8] Ita Gidauniyar bata ita rubutawa ko kirkirar bayanai akan shafukan wiki da kanta ba.[9] Sai dai Gidauniyar ta na aiki da mutane masu bada gudummawa da kungiyoyin abokan hulda kamar su Chaptocin Wikimedia, thematic organizations, user group da dai sauran abokan aiki daga Kasashen daban daban na duniya, kuma ta yi alkawari acikin kudirinta cewa zata gabatar da bayanai na ilimi masu amfani daga shafukanta ga al'umma kyauta a yanar gizo don wanzuwa na har abada.[10]
Wikimedia Foundation ta samu ikon sashe 501(c)(3) daga dokar Internal Revenue Code ta Tarayyar Amurka amatsayin ta takasance na taimakon alumma a shekarar 2005.[11] Lambar National Taxonomy of Exempt Entities (NTEE) code shine B60 (Adult, Continuing education).[12][13] Dokokin foundation ya bayyana jawabin dan karba da farfado da bayanai akan ilimi ta bayar dashi ta hanyar daya dace ga duniya baki daya.[14]
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads