Wikipidiya

From Wikipedia, the free encyclopedia

Wikipidiya
Remove ads

Wikipidiya Insakulofidiya ce ta kyauta da ke tattare da harsuna daban-daban a faɗin duniya, wanda al'ummomi masu bada gudummawa ke rubuta mukalai ta hanyar haɗin gwiwa a fili (ba tare da ɓoye-ɓoye ba). A turance a na kiran editocinta da suna Wikipedians. Wikipidiya ta kasance farfajiyar nazari mafi girma a tarihin ilimin duniya.[1] Ta kasance ɗaya daga cikin fitattun shafukan yanar gizo guda goma a duniya kamar yadda Similarweb ta zayyano; izuwa shekara ta 2022 kuwa, Wikipidiya itace ta 7 a cikin jerin fitattun shafuka na yanar gizo a duniya.[2][3][4] gidauniyar Wikimedia Foundation ce ke daukan nauyin shafin wikipidiya. ita kuwa Wikimedia Foundation wata kungiya ce wanda ba'a samar da riba (wato non-profit organization a Turance) na kasar Amurka, kuma suna samun kudadensu ne ta hanyar taimako/gudummawa (donation) daga wasu kungiyoyi ko jama'a.[5]

Thumb
tambarin shafin Wikipedia
Thumb
Jimmy Wales babban shugaban Wikipedia kuma wanda yasamar da Manhajar
Thumb
Larry Sanger mutum na biyu da suka ƙirƙiri Manhajar Wikipedia
Quick facts URL (en), Eponym (en) ...
Thumb
Banner nan Wikipedia

Wikipedia shafi ne na yanar gizo wanda masu bada gudummawa ke rubuta muƙalai kuma su ke gudanar da ita, ta hanyar shigar da ilimi ko gyare-gyare da sauransu. A Turance ana kuma kiran duk wani mai gyare-gyare ko shigar da ilimi a shafukan Wikipedia da suna "Wikipedian". Wikipidiya tana tattare da harsunan duniya da dama, a shafinta kowa na iya ƙirƙira ko gyara muƙala a kyauta domin taimakawa wajen samar da ilimi kyauta, wannan ne yasa wikipidiya tayi zarra a duk duniya wurin samar da ilimi daga asalin inda ilimin ya fito.

Kowa da kowa na da damar bada gudummawa wajen yaɗa ilimi ta hanyar ƙirƙiran sabuwar muƙala ko gyara ƙirƙirarrun muƙalai da ke buƙatan a ingantasu ta hanyar gyara wasu 'yan kura-kurai ko ƙarin bayani. Harwayau babu wani shafi a duniya baki ɗaya da ya tattara ilimi da bayanai a yanar gizo a yanzu kamar wikipidiya, kuma miliyoyin ɗalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga manhajar a kullum.

Remove ads

Tarihi

An ƙaddamar da shafin Wikipidiya ne a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2001, Jimmy Wales tare da Larry Sanger ne suka haɗa gwiwa wajen samar da shafin. Suka sanya mata suna ta hanyar hade kalmar wiki da encyclopedia. A farkon ƙirƙirar shafin an kafa tane da Turanci kadai amma daga baya sanadiyar karɓuwa da shafin yayi ne yasa ake samar da ƙarin Harsuna akai-akai har zuwa yanzu. A halin yanzu akwai maƙaloli sama da 6,713,721 a sashen Wikipidiya na Turanci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne shahara da tarin maƙaloli. Ayanzu akwai sama da maƙaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka sama da 301, sannan shafin yana samun masu ziyara mabanbanta sama miliyan 500, adadin duka masu ziyara sunkai sama da biliyan 18 ko wanne wata tun daga watan Fabrairu na shekara ta 2014.

Remove ads

Hausa Wikipidiya

A sashen Hausa na wikipidiya kuma akwai maƙaloli sama da dubu 53 ya zuwa watan Janairu a shekara ta 2025.[6] duk da yake sashen yana da ƙarancin masu bayar da gudunmuwa amma a hankali sashen yana ƙara bunƙasa cikin gaggawa.

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads