Zubby Michael
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Zubby Azubuike Michael Egwu wanda aka fi sani da Zubby Michael (an haife shi a ranar 1 ga Fabrairun 1985 a Jihar Anambra, Najeriya ) ɗan wasan fina-finan Najeriya ne kuma mai shirya fina-finai. An san shi da rawar da ya taka a cikin Three Windows, Royal Storm da Lady Professional.[1][2] Fitowarsa ta farko a fim din mai suna Missing Rib amma an san shi da gwauraye uku inda ya taka rawa.[3][4]
Remove ads
Rayuwa da aiki
An haifi Zubby a ƙaramar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra a ranar 1 ga watan Fabrairun 1985 amma ya girma a Adamawa inda ya yi karatun firamare. Ya halarci Jami'ar Nnamdi Azikiwe inda ya samu digiri na ilimin aikin jarida[5]
Ya fara wasan kwaikwayo a Yola tun yana matashi. Fitowarsa na farko na fim yana cikin fim mai suna Missing Rib amma ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim ɗin The Three Windows.[6] Zubby ta fito a wasu fina-finai da dama.[7][8]
Sana'ar siyasa
A ranar 25 ga Nuwamba, 2019 an naɗa shi muƙamin siyasa a matsayin mai ba gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano shawara na musamman kan harkokin yada labarai.[9][10] An ba shi takardar shaidar karramawa ne saboda gudunmawar da ya bayar ga shirin karfafa matasa a gidan rediyon City 89.7 fm a jihar Anambra.
Remove ads
Kyaututtuka da zaɓe
Ayyukan Ayyuka
Remove ads
Hotuna
Tambayoyi
Fina-finai
Remove ads
Nassoshi
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads