Rikicin Jammu da Kashmir (Indiyanci: कश्मीर विवाद, Urdu: مسئلہ کشمیر‎) takaddama ce ta yanki a tsakanin kasashen Indiya da Pakistan. Indiya tana ayyana dukkan yankin da nata ne. A yanzu kuma tana da iko da kashi 43% na yankin, wanda ya hada da yankin Kashmir, Ladakh da kuma Siachen Glacier. Yayinda itakuma kasar Pakistan take da iko da kaso 45% na yankunan Jammu da Kashmir, wanda suka hada da yankunan Azad ta Kashmir da kuma yankunan arewacin Gilgit da Baltistan. Pakistan tace yakamata yayi zaben raba gardama a Kashmir domin tabbatar da samun ra'ayin jama'ar yankin akan kodai ya kasance a Pakistan ko Indiya ko kuma yasamu gashin kan sa.[1] [2]


Tarihin rikicin Kashmir

Rikicin ya fara ne lokacin da ake neman bangarewar kasar Indiya a (1947-47). A watan Oktoba 20, 1947, kabilu daban daban suka kokanta da mamayar da kasar Pakistan ke yi a yankunan Kashmir. Da farko dai Maharaja na Jammu da Kashmir ya fara yakar hakan amma ranar 27 ga Oktoba yayi korafi ga babban gwamna na mulkin mallaka wato Louis Mountbatten. Wanda ya amince da hakan, bayan an saka hannu a kan takardun tallafawa Indiya wajen korar sojojin Pakistan ne sai sojojin Indiya suka shiga yankunan na Jammu da Kashmir da umarnin cewa a dakatar da kowanne irin ayyuka na Pakistan a yankunan. Haka kuma Indiya ta kai al'amarin ga Majalisar Dinkin Duniya. Kuma dai ita Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kira ga Pakistan data gaggauta da barin yankunan amma kuma ita Pakistan din taki amincewa. A 1947-8 Indiya da Pakistan suka yi yaki karon farko a tsakanin su akan Jammu da Kashmir.

Ruwa

Wani karin dalilin da ya kawo rikicin na Jammu da Kashmir kuma shine Ruwa. Mafiya yawancin kogunan yankunan suna farawa ne daga Kashmir. Wasu daga cikin suna suna haduwa ne a babbar madatsa ta Kogin Indus, kamar su kogunan Jhelum da Chenab. Sune suke wucewa su shiga kasar Pakistan kuma mutane nayin amfani da shi wajen noman rani. Sauran kogunan kamar na Ravi, kogin Beas da na Sutlej suna shiga zuwa arewacin Indiya.

Wani kari daga dalilin haddasuwar rikicin shine Iyaka a 1947, Indiya ce ke iko da mafiya yawancin filayen noman ranin mutanen Pakistan. Kuma kasar ta Pakistan tana fargabar watarana Indiya kan dates hanyoyin ruwan da suka faro daga yankunan da Indiya ke da iko a Kashmir. Wannan kuma kan cutar da tattalin arzikin Pakistan. Anyi yarjejeniya ta ruwan Indus wadda aka sama hannu a 1960 domin daidaita rabon Ruwa.[BBC HAUSA, Rikicin Kashmir 1]

Halin yanzu

Thumb
Yansanda da masu zanga zanga na fuskantar juna a Kashmir watan Disamba 2018

A yau Kashmir ta kasu kamar haka:

Jamhuriyyar Indiya na iko da yankin Jammu da Kashmir. Wanda ya hada da yankunan Jammu, Kashmir da Ladakh. Pakistan na daukar hakan da yankin da Indiya ke da iko a Kashmir. Yankunan Arewacin Azad Jammu da Kashmir Pakistan ce ke tafiyar da ikon su. Islamabad na kiran su da yankunan Kashmir wanda Pakistan ke da iko. Indiya kuwa na kiran su da yankunan Kashmir da Pakistan ta mamaye.

Yankin da ake kira Aksai Chin kuma kasar Sin ce keda iko da shi. Sannan kuma Sin din tana da iko da yankunan da ta karba daga hannun Pakistan, suna kiran su da Karokoram.[3]

Manazarta

Wikiwand in your browser!

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.

Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.