Katsina (jiha)

Jiha ce a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia

Katsina (jiha)
Remove ads

Katsina jiha ce a shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya.[1] An kuma ƙirkiri jihar Katsina ne a shekarar 1987, lokacin da aka samar da ita daga jihar Kaduna. A yau, Jihar Katsina ta yi iyaka da Jihohin Zamfara da Kaduna da Kano da Jigawa, har ila yau Kuma Katsina tanada iyaka da Jamhuriyar Nijar. Ana yi mata laƙabi da "Ta Dikko Ɗakin Kara", kuma ana yi wa Katsinawa kirarin "Kunya gareku ba dai tsoro ba". Babban birnin jihar da garin Daura, an bayyana su daga cikin "tsofaffin mazaunun al'adu da Musulunci da kuma ilmantarwa" a Najeriya.

Quick facts Wuri, Babban birni ...
Thumb
Thumb
Katsina State Inland Revenue Office, Katsina City
Thumb
Fadar sarkin katsina
Thumb
Gobarau minaret katsina

Jihar Katsina, tana da mazauna har sama da 5,800,000 a ƙidayar shekarar dubu biyu da shidda (2006). Jihar Katsina ce ta biyar (5) mafi girma acikin Jerin yawan haɓakar jama'a a jihohi biyar mafi girma a cikin ƙasar ta Nijeriya, cikin yawan jama'a, duk da kasancewarta ta bakwai daga cikin Jihohi 17 mafi faɗin ƙasa daga cikin jihohi 36 na tarayyar Najeriya. Ta fuskar adadin ƙabilu kuwa, jama'a, Fulani sun fi kowace ƙabila yawa a jihar, kuma mafi yawancin mutanen Jihar Katsina suna bin koyarwar addinin Musulunci. A shekarar 2005, [2] A shekarar 2005,[3][4]Katsina ta zama jiha ta biyar a Najeriya da ta yi amfani da tsarin Shari'ar Musulunci.

Gwamnan jihar Katsina na yanzu shi ne Dr.Dikko umar radda, dan jam’iyyar "All Progressives Congress"Ana ɗaukar Jihar a matsayin babbar cibiyar siyasar Muhammadu Buhari, ɗan asalin garin Daura, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019 da kusan kashi 80% na ƙuri’un mutanen jihar. [5]

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin Jihohin Najeriya da ke fama da matsalar ta'addanci. Wacce ta fara a shekarar 2020. Kungiyar yan ta'adda da yan fashi da garkuwa da mutane sun yi garkuwa da yara sama da 300 a ƙaramar hukumar kankara.[6][7]

Remove ads

Demography

Fulani sun fi kowace kabila yawa.[2]

Addini

Galibin mutanen Jihar Katsina musulmai ne,[8][9]Samfuri:Fix-span The Church of Nigeria has a Diocese of Katsina.[10] kuma Gobarau Minaret muhimmin gini ne a birnin Katsina (kuma tarihi ya tabbbatar da cewa an ginata ne domin amfanin addinin musulunci). Jihar Katsina, har yanzu tana aiwatar da Shari'a a duk faɗin jihar. Akwai kuma Cocin na Najeriya yana da Diocese na Katsina. Cocin Redeemed Christian Church of God da Cocin Roman Katolika suna nan a cikin jihar.[11]Samfuri:Failed verification[12]

Remove ads

Kananan hukumomin

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads