Ken Saro-Wiwa

From Wikipedia, the free encyclopedia

Ken Saro-Wiwa
Remove ads

Kenule Beeson "Ken" Saro-Wiwa (an haife shshi a ranar 10 ga watan Oktoba 1941 - 10 Nuwamba 1995)[1] ya kasance marubuci ɗan Nijeriya, mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, mai rajin kare muhalli, kuma ya ci kyautar ''Kyauta ta Rayuwa'' jajirtacce kuma abin misali wajen yin gwagwarmaya ba ta tashin hankali ba don farar hula, tattalin arziƙi da muhalli haƙƙoƙi da kuma Kyautar Muhalli ta Goldman.[2] Saro-Wiwa ya kasance memba ne na mutanen Ogoni, kabilu marasa rinjaye a Najeriya wadanda asalin garinsu, Ogoniland, a yankin Neja Delta an yi niyyar hako danyen mai tun daga shekarun 1950 wanda ya gamu da mummunar illa ta muhalli daga shekaru da dama na zubar da dattin man fetur ba tare da ƙa'ida ba.[3]Tun da farko a matsayin kakakin ƙungiya sannan kuma a matsayin shugaba na Movement for the Survival of the Ogoni People (MOSOP), Saro-Wiwa ya jagoranci kamfen ne na nuna adawa da lalata muhalli na kasa da ruwan Ogoni da ayyukan kamfanonin mai na kasa da kasa, musamman ma kamfanin Royal Dutch Shell.[4] Ya kuma kasance mai sukar lamirin gwamnatin Nijeriya, wanda ya ke kallo a matsayin mara son aiwatar da dokokin muhalli a kan kamfanonin man fetur na kasashen waje da ke aiki a yankin.[5]

Quick facts Rayuwa, Haihuwa ...
Thumb
Bus Memorial to Ken Saro-Wiwa
Thumb
An fitar da wasiƙar daga tsare sojoji zuwa ga ma'aikaciyar haɗin kai Majella McCarron, 1 Oktoba, 1994



Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads