Moroko
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Maroko ko Moroko Larabci المغرب , (Al-Magrib) (ma'ana mafadar rana ko yamma). A yaren Abzinawa, kuma ⵍⵎⵖⵔⵉⴱ Faransanci Moroc, cikaken sunan ƙasar shine Masarautar Maroko. da yaren Abzinanci ko kuma Berber ⵜⴰⴳⵍⴷⵉⵜ ⵏ ⵍⵎⵖⵔⵉⴱ da Larabci kuma المملكة المغربية Al-mamlaka al-magrabiyya ƙasa ce dake, bin tsarin mulki salon sarauta dake Arewacin Afrika. Ƙasa ce ta asalin yan ƙabilar Abzinawa.


Ƙasar Maroko ta kasance tana da dogayen tsaunuka da kuma Sahara. Ƙasar ta yi iyaka da tekun mediterranean daga Arewaci, sai kuma tekun Atlantic daga yamma, sai kuma wajen ƙasar tayi iyaka da ƙasar Aljeriya daga Gabas.

Al'ummar ƙasar Maroko yakai kimanin miliyan talatin da bakwai (37 million) kuma tana da adadin fadin ƙasa kimanin da yakai kilomita (710,550) (sukwaya mil 172 410). Babban birnin tarayyar ƙasar shine Rabat, kuma birni mafi girma a ƙasar shine Kasablanka. Sauran birane masu girma sun haɗa da Marrakeah, Tangier, Sale, Fea da kuma Meknes.[1][2]
Remove ads
Hotuna:



- Assilah
- Birnin Casablanca
- Coat of Arms
- Tutar kasar
- Hamadan sahara cike da rakuma a cikin kasar Maroko
- Kyawun sahara ada tsakar rana
- Gida a bakin teku a kasar Maroko
- Takalman gargajiya a kasar Maroko
- Kasar Maroko a shekaran 1860
- A'ada a kasar Maroko
Yaren Berber ko Abzinanci shine babban yare kuma mai asali a ƙasar kafin Larabci da ya shigo bayan mamayar da larabawa sukayi ma ƙasar. Musulunci ne babban addini na kasar.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads