Muhammad Yunus Jaunpuri

From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Muhammad Yunus Jaunpuri (an haife shi a watan Oktoban shekarata1937 kuma ya mutu a ranar 11 ga watan Julin 2017) ya kasance malamin Hadisi na Islama na Kasar Indiya, kuma tsohon Shaykh al-Hadith na Mazahir Uloom, Saharanpur. Yana daga cikin manyan dalibai da almajiran Muhammad Zakariyya Kandhlawi.

Quick facts Rayuwa, Haihuwa ...
Remove ads

Tarihin rayuwa

An haifi Jaunpuri a ranar 2 ga Oktoban shekarar 1937 a Jaunpur. Ya kammala karatu daga Mazahir Uloom, Saharanpur a shekara ta 1961. [1]

Jaunpuri ya koyar da littattafan Hadisi daban-daban a cikin Mazahir Uloom, Saharanpur. An nada shi a matsayin Shaykh al-Hadith na Jamia a shekara ta 1388 AH. Ya karantar da Sahih Al-Bukhari a cikin Mazahir Uloom, Saharanpur kusan shekaru 50. Daliban sa sun hada da Yusuf Motala da Abdur Raheem Limbada.[ana buƙatar hujja]

Jaunpuri ya mutu a ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2017. Mutane sama da miliyan daya ne suka halarci jana’izar sa kuma Talha Kandhlawi, dan Muhammad Zakariyya Kandhlawi ne ya jagoranci addu’ar. Babban malamin addinin Islama na duniya Ismail ibn Musa Menk ya nuna alhinin rasuwarsa. Shima mawakin Indiya kuma masani Fuzail Ahmad Nasiri ya nuna alhininsa kuma ya ce Jaunpuri fitaccen malamin hadisi ne.[2][3][4][5]

Rayuwar mutum

Jaunpuri bai zabi yin aure ba kuma ya kasance bai da aure a tsawon rayuwarsa. Fuzail Ahmad Nasiri ya ce an ambaci dalilai da dama na hakan amma mafi alherin shi ne Jaunpuri bai ga ya iya yin aure ba don haka ya kasance ba shi da aure. Ya ji damuwa da baƙin ciki don ba shi da yara.

Remove ads

Ayyukan adabi

Littattafan Jaunpuri sun hada da:

  • Al-Yawaqit al-Ghaliyah
  • Kitab at-Tauhid
  • Nawadir al-Hadith
  • Nibrās al-Sārī ilā Riyāḍ al-Bukhārī
  • Nawadir al-Fiqh

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads