Umar II
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Umar bn Abdil-Aziz ( Larabci: عمر بن عبد العزيز, romanized: ʿUmar ibn ʿAbd al-ʿAzīz ; 2 Nuwamba 680 – c. 5 February 720 ), wanda aka fi sani da Umar II ( عمر الثاني ), shi ne halifan Umayyawa na takwas . Ya bayar da gagarumar gudunmawa da gyara ga al’umma, kuma an bayyana shi a matsayin “Mafi tsoron Allah da ibada” a cikin sarakunan Banu Umayyawa kuma ana kiransa da Mujaddadi na farko kuma khalifan Musulunci na shida. [1]
Ya kuma kasance dan uwa ga tsohon halifan, kasancewarsa dan kanin Abdul-Malik, Abd al-Aziz . Ya kuma kasance jikan halifa na biyu, Umar ibn Al-Khattab .
An kewaye shi da manyan malamai, an ba shi umarni da ya tattara hadisai na farko a hukumance da kwadaitar da ilimi ga kowa da kowa. Ya kuma aika da jakadu zuwa kasashen Sin da Tibet inda ya gayyaci sarakunansu da su karbi Musulunci . sannan kuma ya kasance yana da hakuri da ‘yan kasa wadanda ba musulmi ba. A cewar Nazeer Ahmed, a zamanin Umar bn Abdil-Aziz ne addinin Musulunci ya samo asali kuma ya samu karbuwa a wajen dimbin al'ummar Farisa da Masar .
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads