From Wikipedia, the free encyclopedia
Olukayode Ariwoola (an haife shi a ranar 22 ga watan Agusta shekara ta 1954) masanin shari'a ne ɗan Najeriya kuma mai shari'a na Kotun Ƙoli ta Najeriya wanda ke riƙe da muƙamin babban alƙalin alƙalai na Tarayyar Najeriya. A da ya kasance Alƙalin Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, sai kuma a ranar 22 ga watan Nuwamba, shekarar 2011, aka naɗa shi a benci na kotun ƙolin Najeriya a matsayin mai shari’a, wanda babban jojin Najeriya ya rantsar da shi.[1][2] An naɗa shi yana jiran amincewar Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin babban Alƙalin Alƙalan Najeriya a ranar 27 ga watan Yunin 2022 bayan murabus din Alƙalin Alƙalan Najeriya Tanko Muhammad.[3][4][5][6][7][8]
Olukayode Ariwoola | |||
---|---|---|---|
27 ga Yuni, 2022 - ← Tanko Muhammad | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 22 ga Augusta, 1958 (65 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Obafemi Awolowo | ||
Matakin karatu | Bachelor of Laws (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Lauya |
An haifi Ariwoola a garin Iseyin na jihar Oyo, ya fara karatun firamare ne a makarantar Local Authority Demonstration School da ke Oluwole a karamar hukumar Iseyin ta jihar Oyo. Daga nan ya wuce Makarantar Zamani ta Musulmai a wannan Garin daga shekarar 1968 zuwa shekarar 1969. Sannan ya halarci makarantar Ansar-Ud-Deen da ke Shaki ta Jihar Oyo inda ya kammala Sakandare. Ariwoola ya kammala karatunsa na jami'a, a Jami’ar Ife (Jami’ar Obafemi Awolowo a yanzu), a Ile Ife, Jihar Osun inda ya samu digirinsa na farko a fannin shari’a (LLB).
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.