Diego Maradona

From Wikipedia, the free encyclopedia

Diego Maradona
Remove ads

Diego Armando Maradona Franco (lafazi|ˈdjeɣo maɾaˈðona, an haife shi a ranar 30 ga watan Oktoban Shekara ta 1960), tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Argentina, kuma mai kula da Mexican second division club Dorados. Yawancin masu harkokin wasanni, da suka hada da marubuta wasan ƙwallon ƙafa, yan'wasa, da magoya baya, na ganinsa amatsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan ƙwallon ƙafa a Duniya. Yana ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallon ƙafa na FIFA na ƙarni na 20 tare da Pelé.[1][2] Yanayin Kallo, bayar da ƙwallo da yadda Maradona yake sarrafa Ƙwallon sa shine ya bambanta shi da sauran Ƴan Ƙwallo. Hakanan ma ƙwarewar sa wajen haɗa kan ƴan wasan ƙungiyar sa a yayin da ake buga ƙwallon shima ya ƙara masa ƙima sosai. Ana yi masa laƙani da "El Pibe de Oro" ("Yaron ƙwarai"), sunan da ya ɗauka shiga a tarihin tashen sa na ƙwallon ƙafa.[3].

Quick facts Rayuwa, Cikakken suna ...
Thumb
hoton Dan kwallo maradona
Thumb
hoton maradona
Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads