Iyabo Ojo
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Alice Iyabo Ojo (an haife ta ranar 21 ga Watan December a shekara ta alif 1977) yar Najeriya ce, yar'fim, mai'shiri da samar da fim.[1][2][3][4] Ta fito acikin sama da 150 na fina-finai, Kuma ta shirya fim 14 da kanta.[1]

Remove ads
Farkon rayuwa da karatu
Iyabo Ojo an haife ta ne da suna Alice Iyabo Ogunro a ranar 21 ga watan Disamba, shekara ta alif 1977, a Lagos, Najeriya, dukda mahaifin ta daga Abeokuta, Jihar Ogun yake.[5] Itace karama daga cikin su uku, sauran yayyin ta biyu maza ne.[5] Tayi makaranta a Lagos National College, Gbagbada, bayan kammalawa ta wuce ta karanta Estate Management a Lagos State Polytechnic.[6]
Aiki
Iyabo Ojo tafara shirin tun a secondary school, Iyabo Ojo sannan a shekara ta 1998, tafara shirin fim na farko. Ta yi rijista da Actors Guild of Nigeria (AGN) da taimakon Bimbo Akintola, sannan kuma tayi kokarin kafa alaka da wasu mutane [7]
Ojo ta rubuta da fitowa acikin fina-finan Najeriya da dama. Fim dinta n'a farko shine a 1998's Satanic, wani fim din turanci. In 2002, ya kuma yi fim din Yarbanci tare da Baba Darijinwon.[8] A watan Janairun shekarar 2015, fim din ta mai suna Silence, wanda ya fitar da Joseph Benjamin Alex Usifo, Fathia Balogun, da Doris Simeon, kuma an nunnuna a Silverbird Cinemas, Ikeja, a Lagos.[9][10]
A shekarar 2004, Ojo ta fara shirya fina-finan ta. Fim din farko na Ojo shine Bolutife, sannan ta shirya Bofeboko, Ololufe, Esan da Okunkun Biribiri.[1] Ta kuma raba aurenta da mijinta gabaninta yin sunanta.
Remove ads
Rayuwarta
Ta auri mutumin Lagos wanda ke sana'ar saida fina-finai a shekarar 1999, asanda take shekara 21 da haihuwa,[11] Ta yi hutu daga cigaba da sana'arta. Ta haife yaro namiji sannan ta haifi mace (haihuwarsu a shekarar 1999 da 2001 ajere), na fari Felix Ojo da Priscilla Ajoke Ojo, amma ayanzu ta rabu da mahaifin su.[12][1][5] Ta alakanta rabuwar aurenta na farko da yin aure da wuri da tayi.[13] Ojo tace sunan Ojo na sunan ta sunan tsohon mijinta ne kuma dan Haka tana son tarinqa amfani da sunan Ojo.[11][14]
Gidauniyar Pinkies
Iyabo Ojo ta kaddamar da NGO, Pinkies Foundation, wanda ke kula da bukatun kananan yara masu bukata ta musamman, A watan Mayun shekarar 2011. Ta yi bikin murnar cikar Gidauniyar shekara 5 da samar dashi a ranar 1 ga watan May shekara ta 2016, wanda akayi bikin a R&A City Hotel, Ikeja, Lagos.[15]
Fina-finai
- Satanic (1998)
- Agogo Ide (1998)
- Baba Darinjinwon (2002)
- Okanla (2013)
- Silence (2015)
- Beyond Disability (2015)
- Black Val[16]
- Arinzo
- Apo Owo
- Awusa (2016)
- Tore Ife (Love)[17]
- Trust (2016)[17]
- Ore (2016)
- Ipadabo (2016)[17]
- Twisted Twin (2016)
- Kostrobu (2017)
- Gone to America (2017)
- Divorce Not Allowed (2018)
Duba kuma
- Jerin masu shirya fina-finan Najeriya
- Jerin mutanen Yarbawa
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads