Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango

From Wikipedia, the free encyclopedia

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango
Remove ads

Ƙasar Kwangosunan ta jamhuriyar Kwango, tun kafin zamanin mulkin mallaka, to amma bayan da Turawan mulkin mallaka, suka mamaye kasar sai suka sa mata suna, Jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango, (a ranar 1 ga watan Agustan, shekara ta (1964) kuma an yi haka ne da nufin banbance ta da makwafciyarta wadda ita ma sunanta jamhuriyar Kwango.

Thumb
Jamhuriyar domokaradiyar kwango
Quick facts Kirari, Official symbol (en) ...
Thumb
Tutar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Thumb
taswirar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Thumb
rafin kashiemin a kwagon

Mobutu Sese Seko shine tsohon shugabar kasar na kwango.daga bisani kuma Zayar ta karfi Mulkin,Yadda aka yi ta samu tsohon sunanta na Zayar kuwa ya faru ne a ranar (27) ga watan Oktoban shekara ta (1971) a zamanin mulkin tsohon shugaba Mabutu Sese Seko. Kuma sunan ya samo asali ne daga yadda al'ummar ƙasar Potigal suke kiran kogin kwango da suna nzere ko nzadi, wato ma'ana "Kogi mai haɗiye sauran koguna." To amma bayan da aka gudanar da Yakin Kwango na farko, wanda yai sanadiyyar hambarar da gwamnatin Mobutu a shekara ta (1997) an sake mayar wa da ƙasar sunanta na zamanin Turawan mulki, wato jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango.

Ita dai jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango, kasar Faransa ce tai mata mulkin mallaka, kuma ta kansance ne a yankin tsakiyar Afirka.

Shugaba Denis Sassou Nguesso, na jamahuriyar Kwango Babbar hanyar da ake iya rarrabe kasashen kwangon guda biyu ita ce, ita wannan kwangon da muke batu akai a kodayaushe ana ambatonta ne da jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango, ko a ce DR Kwango, ko DRC, ko RDC, ko kuma a kira ta da Kwango-Kinshasa, wato a jingina mata sunan babban birninta na Kinshasa. Sabanin daya Kwango din da ake mata laƙabi da Kwango-Brazzaville.

Shi dai wannan suna "Kwango" Suna ne na "Kogin Kwango", har ilayauk kuma, akan kira shi da Kogin Zayar (Kuma sunan ya samo asali ne daga sunan wata ƙabilar da ake kira Bakongo). Jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango dai, kasa ce da ta sha amsa sunaye da dama a tarihi, inda kuma akan ce mata 'yantacciyar ƙasar Kwango, ko Kwangon Beljiyom, ko Kwango-Kinshasa, ko kuma Zayar.

Duk da cewa ƙasar ta jamhuriyar dimokuradiyyar ta kasance ne a yankin tsakiyar Afirka, to amma fa ta fuskar harkokin tattalin arziƙi da kuma bangaranci, ta alakanta kanta ne da kasashen Kudancin Afirka kasancewar ita memba ce a kungiyar bunkasa kasashen Kudancin Afirka wato (SADC).

Remove ads

Iyaka da mutane

Thumb
Jamhuriyar domokaradiyar kwango ta kasance ƙasa mai karamcin tattalin arziki a wani lokaci

ƙasar Kango Ita ce ƙasa ta uku a girman taswira a nahiyar Afirka. Sannan kuma kamar yadda kiyasin Majalisar dinkin Duniya ya nunar, kasar na da yawan al'umma kimanin miliyan 66,020,000 wanda hakan ya ba ta iko zama ƙasa ta 19 a jerin kasashe mafiya yawan al'umma a duniya, kuma ta huɗu a yawan al'umma a Afirka, amma kuma a rukunin kasashen da suke magana da harshen faransanci a duniya ita ce kasa ta farko a yawan al'umma. Kasar ta yi iyaka da kasashe tara su ne kamar haka:-

Remove ads

Hotuna

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads