Japhet N'Doram
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Japhet N'Doram (an haife shi a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 1966) ɗan asalin ƙasar Chadi ne kuma tsohon ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba.
Shekaru 14 mafi girma a rayuwarsa ta kwallon ƙafa su ne na wanda ya shafe a tare da Nantes, wanda ya wakilta a matakai da dama. Ana yi masa alkunya da laƙabin Maye. [1]
Remove ads
Tarihin Rayuwa
N'Doram wanda aka haifa a N'Djamena, ya fara ƙwallo ne tare da klub ɗin Tourbillon FC na cikin gida, sannan ya shafe shekaru uku a Kamaru tare da Tonnerre Yaoundé, daya daga cikin manyan kulob a yankin Saharar Afirka . A shekarar 1990 lokacin yana ɗan shekaru 24, N'Doram ya sanya hannu a kungiyar FC Nantes a Faransa, inda ya ci kwallaye biyu a wasanni 19 a kakarsa ta farko a gasar Lig 1 ; samun damar sanya hanu a babban kwantiragin sa na farko ta zo ne a lokacin da Jorge Burruchaga na Ajantina ya tafi hutu saboda ya samu rauni inda a nan ne aka bashi lasisin sa hanu don maye gurbin abokin wasan nasa. [2]
Remove ads
Iyali
Ɗan N'Doram mai suna Kévin, shi ma ɗan ƙwallon ƙafa ne dake taka leda a Monaco. [3]
Ƙididdigar Wasanninsa
- Includes Coupe de France, Coupe de la Ligue, Trophée des Champions
- Includes UEFA Champions League, UEFA Cup
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads