Sunnah

From Wikipedia, the free encyclopedia

Sunnah
Remove ads

Sunnah Shi ne ɓangare mafi girma da tsari daga cikin ɓangarorin addinin Musulunci. Asalin sunan ya zo ne daga kalmar Sunna[1][2][3][4], wato koyi da yin dukkan abun da Annabi Muhammad (S.A.W.) ya aikata, ko ya yi umarni, da a aikata ko kuma aka aikata shi a gabansa amma baiyi hani akan abun da aka aikatan ba. Bambanci tsakanin aƙidun Sunnah da kuma na Shi'a ya samo asali ne tun daga taƙaddama a kan wanda ya cancanci ya jagoranci al'umar Musulmi bayan wafatin Annabi (S.A.W.), wato wanda ya cancanci ya yi Khalifanci. A ɓangaren fahimtar mabiya Sunnah sun ce, tunda yake Annabi (S.A.W) bai yi nuni ba da wani cewa shi za'a bi to sai suka yanke hukuncin a bai wa surukinsa wato Sayyadina Abubakar ya zamo Khalifa na farko.

Thumb
Thumb
Masallacin sunnah
Quick facts Asali, Mawallafi ...
Fayil:Al-Haram mosque-Flickr - Al Jazeera English.jpg
Masallacin Harami dake Makkah waje ne na daya mafi tsarki a wajen Musulmi Mabiyan Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W.)
Thumb

Amma a ɓangaren Mabiya Shi'a kuwa sai suka ce ai a ranar Ghadir Khumm Annabi (s.a.w) ya sanar da cewa ba wanda zai gaje shi sai ɗan'uwansa kuma sirikinsa wato Sayyadina Ali sun ce saboda shi jininsa ne kuma surukinsa wato mijin ƴarsa, Sayyida Fatima "Bint Nabiy".

Tun daga nan ne rikicin ɓangaren Sunnah dana ɓangaren Shi'a ya samo asali.

A shekarar 2009 Musulmai mabiya Sunnah sun kai 87% zuwa 90%. Haka zalika Mabiya Ɓangaren Sunnah su ne ɓangare a Addini wanda suka fi ko wanne yawa a duniya bayan Katolika a addinin Kiristanci. Sanannu ne a sunan da suka yi fice da shi wato Ahlul Sunnah Wal Jama'a wato (al'umma mabiya sunnah).

Remove ads

Aƙidun mabiya Sunnah

Ga jerin aƙidojin Sunnah kamar Haka:

Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya Sunnah

Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya sunnah guda biyar ne sune.

Imani da Allah da Annabi Muhammada (S.A.W.)

Wato mutum ya furta kalmar SHahada kamar haka LA ILAHA ILALLAH MUHAMMAD RASULULLAH ma'ana mutum ya hakikance a ransa cewa BABU WANI ABIN BAUTAWA DA CANCANTA DA GASKIYA SAI ALLAH SANNAN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) BAWAN ALLAH NE KUMA MANZON ALLAH NE.

Tsai Da Sallah

Yin salloli guda biyar a kowacce rana watau a kowane yini da dare.

Da Azumi Watan Ramadan

Sai yin azumin watan Ramadana wato wata na tara a lissafin kalandar Musulunci.

Da Bada Zakka

Shi ne mutum ya cire wani adadi da shari'a ta faɗa na dukiyar sa wadda ta kai nisabi ya bayar da shi ga mabuƙata Zakka saboda Allah.

Aikin Hajji


Idan Musulmi ya kasance yana da dukiyar da takai zai iya biyan ta wajen zuwa Saudiyyah kuma yana da ƙarfin lafiya to Hajji ta wajaba a kansa.

Shika-shikan imani a wajen mabiya Sunnah

Shika-shikan Imani a aƙidar mabiya sunnah guda shida ne, gasu kamar haka.

  • Imani da Allah.
  • Imani da Mala'iku.
  • Imani da Litattafai Saukakku.
  • Imani da Manzannin Allah.
  • Imani da Ranar Kiyama(Ranar Sakamako).
  • Imani da Kaddara(Mai dadi ko mara dadi).

Matsayin Hadisai a wajen mabiya Sunnah

Sanannun litattafan Hadisannan guda shida wato Kutub al-Sittah sune litattan hadisan da mabiya sunnah suka yi imani da gaskiyar hadisan dake cikin su Ga jerin su:

  • Sahih al-Bukhari na Muhammad al-Bukhari.
  • Sahih Muslim na Mislim ibn al-Hajjaj.
  • Sunan al-Sughra na Al-Nasa'i.
  • Sunan Abu Dawud na Abu Dawood.
  • Jami' at-Tirmidhi na Al-Tirmidhi.
  • Sunan Ibn Majah na Ibn Majah.

Amma ba iyakar wadannan kadai bane litattafan da mabiya sunnah suka amince da gaskiyar hadisan dake cikin su ba, akwai wadansu litattafan da dama wadanda suka hada da:

  • Musannaf na Abd al-Razzaq na ‘Abd ar-Razzaq as-San‘ani
  • Musnad na Ahmad ibn Hanbal
  • Mustadrak na Al Haakim
  • Muwatta na Imam Malik
  • Sahih Ibn Hibbaan
  • Sahih Ibn Khuzaymah of Ibn Khuzaymah
  • Sunan al-Darimi na Al-Darimi

Iyalan gidan Annabi (S.A.W.) a mahangar Sunnah

Su ne DUKKAN DANGIN Manzon Allah (SAW) waɗanda sadaka ta haramta garesu, da kuma MATANSA da ZURIYYARSA. Allah ya yarda da su gaba ɗaya. Sabanin AkidunShi'a ko Rafidanci Wadanda suke cewa Iyakacin Nana Fatima da Imamuna Aliyu da suran zurriyar su,sune kadai Iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.). Wannan gurguwar fahimta ce a mahangar Mabiya Sunnah.

Ahlus Sunnah sun yi ITTIFAQI akan WAJABCIN Son Ahlul Baiti, da kuma HARAMCIN Cutar dasu,ko Munana musu,da magana ko aiki.

Remove ads

Sahabbai a mahangar mabiya Sunnah

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads