Tecno Mobile

Kamafani wayar hannu From Wikipedia, the free encyclopedia

Tecno Mobile
Remove ads

Tecno Mobile kamfanin ƙera wayoyin hannu ne na ƙasar Sin da ke Shenzhen, China.[1] An kafa shi a shekara ta 2006. Wani reshe ne na Transsion Holdings.

Quick Facts Bayanai, Iri ...
Thumb
Techno kamfani
Thumb
tambarin waya na Techo

Kamfanin na Tecno ya mayar da hankali kan kasuwancinsa a majiyoyin Afirka, Gabas ta Tsakiya, Kudu maso Gabashin Asiya, Kudancin Asiya, Latin Amurka, da kasuwannin Gabashin Turai.

Remove ads

Tarihi

A cikin shekara ta 2006, an kuma kafa kamfanin Tecno Mobile a matsayin Tecno Telecom Limited, amma daga baya ya canza suna zuwa Transsion Holdings tare da Tecno Mobile yana aiki a matsayin ɗaya daga cikin rassansa. A cikin 2007, kamfanin Tecno ya ƙirƙiri tambari na biyu, Itel wanda aka sayar a Afirka. A farkon 2008, Tecno ya mayar da hankali ga Afirka gaba ɗaya bayan binciken kasuwa, kuma zuwa 2010, yana ɗaya daga cikin manyan samfuran wayar hannu guda uku a Afirka.[2]

A cikin 2016, Tecno ya shiga dillancin wayar hannu na kamfanin a Gabas ta Tsakiya.[3] A cikin 2017, ya shiga kasuwannin Indiya, inda ya ƙaddamar da samfurin wayoyinsa na 'Made for India': jerin 'i' - i5, i5 Pro, i3, i3 Pro da i7. Kamfanin ya fara dillancin sa a jihohin Rajasthan, Gujarat, da Punjab, kuma a watan Disamba 2017 ya bazu a faɗin kasar.

Kamfanin ya gano wasu kasuwanni masu tasowa, ban da Afirka da Indiya, masu yawan jama'a amma akwai ƙarancin cinikayya hajar sa a wuraren. Har wayau bai tsaya nan ba, ya kutsa kasuwannin Bangladesh da Nepal a cikin 2017 kuma ya fara gwajin sayar da hajarsa a Pakistan.[4] Har yanzu kamfanin na ƙoƙarin kutsawa cikin kasuwar Pakistan kuma ya fara siyar da hajarsa ta yanar gizo-(online) ta hanyoyin kasuwanci ta Intanet-(E-commerce).

Remove ads

Wayoyin da ake ƙerawa

Wayoyin hannu na Tecno da ake sayarwa a Indiya, ana ƙera su a masana'antar Noida (U.P.).[5]

Manazarta

Hanyoyin haɗi na waje

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads