Imam Abu Hanifa

From Wikipedia, the free encyclopedia

Imam Abu Hanifa
Remove ads

Abū Ḥanīfa al-Nuʿmān b. Thābit b. Zūṭā b. Marzubān (larabci|أبو حنيفة نعمان بن ثابت بن زوطا بن مرزبان; Yarayu daga shekara ta c. 699 zuwa shekara 767 CE), An haife shi a shekara ta 699 (80 Hijri)
garin Kufa, Umayyad Caliphate, ya kuma rasu a shekara ta 767 (150 Hijri)
a birnin Baghdad, Abbasiyya, Dan asalin Parisa ne shi[1][2][3][4] Shi Dan garin Kufa ne[1]

Thumb
Quick Facts Rayuwa, Cikakken suna ...
Thumb
Portraits of the Imāms Ḥasan (d. 670), Ḥusayn (d. 680), Shāfi`ī (d. 820) and Abū Ḥanīfa (d. 767), with `Abbāsid revolutionary Abū Muslim (d. 755)
Thumb
Abu Hanifa


Ya shahara a karantar da fahimtar sa akan Istihsan, ya wallafa shahararren littafin nan wato Al-Fiqh al-Akbar. Malamansa sune; Hammad bin Abi Sulayman,[1] Ata' ibn abi rabah, Zayd ibn Ali, Ja'far al-Sadiq, da sauran manyan tabi'ai, yakarantar da dalibansa kamar su; Imam Malik Ibn Anas, Imam Al-Shafi'i, Muhammad al-Shaybani, Abu Yusuf, al-Tahawi, Ahmad Sirhindi, Shah Waliullah da sauransu.


Anfi saninsa da Abū Ḥanīfa ko kuma Imam Abū Ḥanīfa musamman a wurin mabiya Sunnah,[5] Yakasance dan karni na 8th ne, mabiyin Sunnah, Malamin Tauhidi kuma Alkali wanda asalinsa ba Parise ne.[6] shine yasamar da makarantar Hanafiyya ko Hanafi Mazhab, wanda har wayau itace Mazhabar dake da mafi yawan mabiya ahlus-sunnah a duniya. [6] Ana kiransa da al-Imām al-aʿẓam ("The Great Imam") and Sirāj al-aʾimma ("The Lamp of the Imams") a wurin mabiya ahlus-sunnah.[6][3]

An haife shi daga cikin Gidan musulunci a garin Kufa,[6] Abu Hanifa yatafi zuwa yankin Hejaz dake kasashen larabawa a waccan lokacin yayinda yake matashi, a nan ne yayi karatu a wuraren manyan malaman garin Makkah da Madina.[6] A matsayin sa na Malamin akida kuma mai hukunci Abu Hanifa yayi suna akan yardarsa da amfani da hankali wurin yin hukunci da ma akida (faqīh dhū raʾy).[6] makarantar Abu Hanifa itace ta zama zuwa makarantar Maturidi school of orthodox Sunni theology.[6]

Al'umman Zaydi Shi'a suma dai baa barsu abaya ba, Dan suna matukar girmama Imam Abu hanifa a matsayin wani babban Malamin addinin musulunci.[7]

Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads