Saudi Arebiya

Ƙasar Saudi Arebiya From Wikipedia, the free encyclopedia

Saudi Arebiya
Remove ads

Saudi Arebiya ko Saudiyya: ƙasa ce da take nahiyar Gabas ta Tsakiya a Duniya. Kasar Saudiya ta kasance ne a nahiyar Asiya, ta kuma kasance fitacciyar kasa a duniya musamman ta bangaren addinin musulunci, kasantuwar addinin musulunci ya zo ne ta hannun Annabi Muhammad (S. A. W) da yake a wannan yanki, hakama a tattalin arziki, Allah ya azurta ƙasar da dimbin arziki da ma'adinai musamman arzikin man fetur. Kasar Saudiyya ta kasance ita ce kasar da ta fi kowacce kasa arzikin man fetur a fadin Duniya. Lallai kasar Saudiya ta kasance kasa ce wacce take da Sahara. Kasar na da mafi yawan bishiyoyin Dabino, kuma su kan noma alkama da Inabi kuma suna daya daga cikin manyan kasa wurin noman gyadar itacen Almond wanda ake mai na gashi, da kuma Madaran Almond, haka kuma kasar Saudiya na noman itacen zaitun watu Olive a turanchi da kuma sauran su. Harshen yan kasar ta kasance Larabci, wanda shine yaren kasar, kuma musulmai daga sassa daban daban na duniya sukan je domin su aiwatar da ibadun su a kasar, kamar aikin hajji da umra. [1]

Thumb
saudi mecca
Thumb
tutar saudi
Thumb
tutar saudi
Thumb
saudi, oman
Thumb
manunin saudi
Quick facts Take, Kirari ...
Thumb
Masu sarautar saudiya
Thumb
Yarima Named bin Abdullahi bin Saudi bin xudeyr na saudiyya kenan
Thumb
saudi

[2]

Remove ads

Addini

Thumb
Dakin ka'aba na garin Makkah mai Alfarma
Thumb
Musulmai masu aikin hajji a masallaci a kasar saudiyya

Kasar saudiya kasa ce ta musulunci, wanda a cikinta ne aka aiko annabin karshe, wato Annabi Muhammad(tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi). Duk shekara miliyoyin Mutane ne suke kai ziyara kasar daga kasashen duniya daban-daban domin aikin hajji mai alfarma da Umrah. Haka kuma kasar Saudiya Arabiya ba a barta a baya ba wurin fannin tsaro ya kasance 23 cikin 145 daga cikin kasashen da aka yi la'akari da su wurin gwajin. karfin sojoji ta duniya na shekara-shekara. Kuma kasar Saudiya Arabiya na daya daga chikin manya manyan kasashen dake fitar da danyen mai. Kuma suna chikin Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur Watu OPEC.

Thumb
Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads