Sallah

Ibadane a musulunci da ake yinshi kulum From Wikipedia, the free encyclopedia

Sallah
Remove ads

Sallah ("bauta", larabci صلاة; jam'i. Larabci صلوات ṣalawāt; ko kuma salat), ko Namāz (نَماز) a wasu harsunan, yana ɗaya daga cikin Rukunnan Musulunci biyar na imani a Islam kuma aikin addini na wajibi akan ko wane musulmi (Mace & Namiji) Taqwa. Aiki ne na Zahiri, mental, da kuma spiritual act na bauta wanda akeyin su sau biyar a rana a waɗansu ƙayyadaddun lokuta (prescribed times). Lokacin yinsa dole mutum ya fuskanci ƙasar Makkah. A aika ce, mai bautan zai tsaya, zaiyi ruku'u, kuma zaiyi sujada, sannan ya kammala yayin da yake zaune a ƙasa.[1] A yayin ko wacce raka'a, mai bautar zai karanta wasu ayoyi daga cikin Ƙur'ani, da yabon Allah da kuma addu'o'i. Kalmar Sallah dai ana fassara ta da bauta, amma kalmar na nufin addu'a ne, shiyasa ma'anar keda rikitarwa. Musulmai na amfani da kalmar "du'a" "ambato" wurin ma'anar kalmar addu'a wanda roƙo ne akeyi ko nema a wajen Allah".

Thumb
yadda ake gudanar da sallah kenan har zuwa sallama
Thumb
Thumb
ruku u yayin salla
Quick Facts Bayanai, Ƙaramin ɓangare na ...
Thumb
Mutane suna Sallah
Thumb
Kallon alƙibla wato ma'aba domin yin sallah
Thumb
Musulmai na sallah sunyi ruku'u
Thumb
Musulmai na sallah

Kafin ayi Sallah sai anyi Alwala. Sallah ta ƙunshi maimaita abu ɗaya ne, da akasani da raka'ah (pl. rakaʿāt ) wanda ke tattare da faɗin wasu ƙayyadaddun kalmomi da jawabai. Adadin wajibcin (fard) raka'o'i rakaʿāt yana tsakanin biyu ne zuwa huɗu, according to the time of day or other circumstances (such as Friday congregational worship, which has two rakats). Sallah wajibi ne akan kowane musulmi face waɗanda suke prepubescent, sukeyin menstruating, ko kuma suke zubar jini a farkon kwanaki 40 bayan haihuwa.[2] Kowace rukuni acikin Sallah ana gabatar da itane tare da yin takbir, wato faɗin (Allahu Akbar) face lokacin tsayawa tsakanin ruku'u da sujada, sannan idarwa dake ɗauke da sallar Musulunci As-salamu alaykum.[3]

Remove ads

Salloli Biyar

Thumb
Dattijon Musulmi lokacin Sallar Zuhur a Masallacin Jama
  • Sallar Fajr (Asubahi),
  • Sallar Zuhr (Azahar),
  • Sallar Asr (La'asar),
  • Sallar Magrib (Martin),
  • Thumb
    Masallaci
    Sallar Isha (Isha'i)

Manazarta

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads