Rundunar Tsaron Nijar

From Wikipedia, the free encyclopedia

Rundunar Tsaron Nijar
Remove ads

Rundunar tsaron Jamhuriyar Nijar (Faransanci Forces Armées Nigeriennes) (F.A.N) ta kunshi rassa na hukumomin tsaron ƙasar, Nijar wadanda suka haɗa da Sojojin Kasar na Nijar,Sojojin saman Nijar, Jandarma,Gardin sarki da Yansandan Nijar.Sojojin kasa da Sojojin sama da Jandarma duka suna karkashin gudanarwar, Ma'aikatar tsaro ta Nijar ne. Yayin da Gardin sarki da Kuma Yansandan Nijar suke karkashin gudanarwar ma'aikatar cikin gida ta Nijar.Dukkannin hukumomin tsaro na Nijar suna samun horon su ne a shiga irin ta hukumar tsaro.Shugaban ƙasar Nijar shine Babban kwamandan tsaro na Nijar.

Quick Facts Bayanai, Gajeren suna ...
Thumb
Thumb
Thumb
Remove ads

Sojojin Kasar Nijar

Duka sojojin kasa da na saman Nijar Shugabannin Soja ne ke tafiyar da gudanarwarsu, wato Shugaban rundunar Sojoji, (Faransanci; Chef d'Etat Major des Armées). Gabaki ɗayansu kuma hukumar hadaka ta shugabannin sojoji ne ke gudanar da su (Faransaci: Etat Major General des Armées). Sannan kuma kowanne reshe na rundunar yanada na shi shugaban. Babban Hafsan hafsoshi na sojojin Nijar shi ne mai bayar da dukkan umarni ga rundunonin tsaro yayin da shi kuma ya ke karbar umarni daga ministan tsaro na kasar wanda shi kuma farar hula ne. Shi kuma ministan tsaron ya na samun na shi umarnin ne kaitsaye daga Shugaban kasa.[1][2]

Sojojin Kasa

Sojojin Kasa na Nijar,runduna ce da ta kunshi dakarun sojan kasa jami'ai 5,200.[3] Akwai rabe-raben na manya da kananan rukuni-rukuni a yankuna da sassa da Jahohi da kuma muhimmai a yankunan Saharaeme[4][1][2]

Tarihi

Thumb
Sojojin Nijar

An kirkiri Rundunar Sojojin Kasa ta Nijar a shekarar 1960.

Hadin gwiwa tsakanin Faransawa da Mutanen Nijar ne suka samar da rundunar sojojin Nijar. A shekarar 1960,yan Afrika goma ne kadai ke da mukaman ofisa a rundunar sojojin Nijar suma duka masu kananan matsayi.

A shekarar 1965 ne shugaba Diori Hamani ya sa hannu kan yar jejeniyar ficewar Faransawa daga rundunar.[5] A shekarun 1970,wata karamar bataliya ta sojojin Faransa suka shiga kasar Nijar.

Kayan yaki

Makamai da motoci da tankokin yaki na rundunar sojojin Jamhuriyar Nijar sun yi karanci matuka kuma raunana ne. Akwai motoci masu silke guda biyu kawai wadanda aka sayo su daga kasar Sin a 2009. Mafiya yawancin motocin yakin sun kai shekaru ashirin ko fiye.[6] Anfi sanin sojojin kasa na Nijar da motocin Languruza 4x4 dauke da bindugu masu tsarbi . Sannan kuma akwai motocin dakon mai da ruwa domin taimakawa wajen kai su ga yankuna masu nisa inda mai da ruwa ke wahala kamar yankunan Sahara.[7].

Motoci

Wannan teburi ne dake nuna motoci na rundunar sojojin jamhuriyar Nijar.

Ƙarin bayanai Suna, Asali ...

.

Remove ads

Sojojin sama

Tarihi

Ankafa rundunar Sojan sama ta kasar Nijar a shekarar 1961.[10]

Tsarin tafiyar da rundunar sojan saman na Nijar, ya kunshi ofishin babban shugaba a hukumar, sai shugabanni na rukunoni, sai bangaren kurtuna da kafatani shugabanni.[11][10]

Horo

zuwa yanzu, babu wata cibiyar bayar da horo ga sojojin saman Nijar. Saidai akwai cibiyar Tondibiah wadda aka kafata domin daukar sabbin kananan ma'aikata da sauran ma'aikatan rassa. Manyan shuwagabanni, matuka jirage da masu gyaran jirage na samun horonsu ne daga kasashen Faransa, Amurika da wadansu kasashe na Kudancin Afrika kamar Moroko da Aljeriya.[9][12]

Remove ads

Jirage

Jiragen yaki na rundunar sosojin sama ta Nijar sun fara bunkasa ne daga shekarar 2008. Sannan suna kara samun tagomashin tallafi daga kasar Faransa da Amurika.[6] Wadannan jirage anfi amfani dasu ne musamman domin gadin iyakoki tun bayan kammala yakin basasa a kasashen Libya da Mali.

Jiragen da ke akwai yanzu

Thumb
Tambarin sojojin saman Nijar daga (1961-1980)
Thumb
Tambarin Sojojin saman Nijar daga (1980-zuwa yau)
Ƙarin bayanai Jirgi, Asali ...

..

Aiyuka a kasashen waje

Thumb
Sojojin Nijar lokacin yaki a kasar ketare

A 1991, Nijar ta aika da jami'an soja 400 domin su tallafa ma kasar Amurika wajen yakin da take yi a kasar Iraki. Hakanan Nijar ta tura da rundunar jami'an ta domin wanzar da zaman lafiya a kasar Côte d'Ivoire. Yazuwa 2003 Rundunar Sojan Nijar ta aiwatar da aiyuka a wadannan kasashen.[14]

Thumb
Sojojon Nijar da motocin yaki dauke da manyan bindugu masu zangon 90mm a lokacin yakin Farmakin Sahara

.

Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads