Libya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Kasar Libya tana daya daga cikin kasashen, dake Arewacin Afirika, kuma tanada iyaka da kasashe guda shida (6) su ne:-

- Daga gabashin kasar, Misra.
- daga kudu maso gabashi, Sudan.






Libya kasar larabawa ce kuma tana daga cikin kungiyar tarayyar Afirika kuma tana daya daga yan kungiyan kasashen larabawa da kungiyar kasashen musulunci, har zuwa yau ita 'yar kungiyar kasashen Arewacin Nahiyar Afirka ce, kuma yar kungiyar kasashen da suke da man fetur ne. Kasar Libya babbar kasa ce a wurin fadin Kasa amma sai dai mafi yawan kasar Sahara ce, Iyakar libya takai 1,759,540 km2 tanada babban iyaka da teku. Shugaban kasar daya shahara shine Muammar Gaddafi.





Remove ads
Tarihi
Libya da harshen misrawan da, wannan suna ya samu ne daga kabilar libo da suke zaune A jihohin da suke tsakanin Misra da Tunisiya.

dadin dadawa, akan kabilar libo kuma da akwai kabilu 'yan asalin Libya kaman Amazik da kabilar feneken. a karni na shida kafin haihuwar Annabi Isah daular kurtaja ta mamaye libya duk da karfinta Romawa sun kwace ta daga hannunsu, a karni na shida bayan haifuwar Annabi isah bizantinawa suka mamaye Libya. Kuma A karni na bakwai bayan haihuwar Annabi Isah sai larabawa suka shigo Libya

.
Libya ta samu ire-iren iko kamar haka:-
- mulkin kafin tarihi.
- lokacin fenekawa da Igregawa da rumawa
- lokacin da Libya tana karkashin mulkin Amauiyawa da abbasiyawa a shekara ta 644
- lokacin mulkin turkawa 1551 zuwa 1911
- lokacin mulkin Italiya 1911 zuwa 1943
- lokacin mulkin Birtaniya da faransa 1943 zuwa 1951
- lokacin samun 'yancin kasa shi kuma ya rabe gida biyu
1 lokacin mulkin sarauta 1951 zuwa 1969
2 mulkin Moammar Gaddafi 1969 har yau Libya ta zama Jamhuriya tin 1977


Remove ads
Mutanen kasar


Mutunen Libya sun kai adadin 6000,000 a sahile a arewacin kasar kabilolin Libya su ne, larabawa, barbarawa, tubawa karaglawa ( hadin turkawa da larabawa ), Buzawa da 'yan tsurarun ( hausawa da bare-bari ).
harshen larabci shi ne harshen kasar, larabcinsu yana da bambanci da sauran na kasashen larabawa kuma da akwai harsuna da yawa masu bambancin harshen ( Amazik, Buzanci tubanci da harshen Hausa ) shi ne harshen kasuwanci a birnin sabha da ke a kudancin kasar .

Remove ads
Addini
- yawancin yan Libya musulmai ne (97%)
- sauran adadin (3%) kawai kiristoci da yahudawa ne.
kuma Libya bata da shi'a samsam mabiya addinin yahudawa ( yahudawa ) yawancin su sun fita daga kasar bayan 1967 a yanzu saura 'yan tsirari a tirbule , Libya tana da 'yan tsirarun kyrke a tirbule da bangazi kuma suna da malamai kyrke daya yana Bangaze da zama
Jihohin Kasar
libya tanada jihohi talatin da biyu sune kamar haka:-
1 Ajdabiya | 17 Ghat | |
2 Al Butnan | 18 Ghadamis | |
3 Al Hizam Al Akhdar | 19 Gharyan | |
4 Al Jabal al Akhdar | 20 Murzuq | |
5 Al Jfara | 21 Mizdah | |
6 Al Jufrah | 22 Misratah | |
7 Al Kufrah | 23 Nalut | |
8 Al Marj | 24 Tajura Wa Al Nawahi AlArba' | |
9 Al Murgub | 25 Tarhuna Wa Msalata | |
10 An Nuqat al Khams | 26 Tarabulus (Tripoli) | |
11 Al Qubah | 27 Sabha | |
12 Al Wahat | 28 Surt | |
13 Az Zawiyah | 29 Sabratha Wa Surman | |
14 Benghazi | 30 Wadi Al Hayaa | |
15 Bani Walid | 31 Wadi Al Shatii | |
16 Darnah | 32 Yafran |
Remove ads
Hotuna
- Tsarin dutse a cikin Tadrart Acacus
- Sahara a Libya
- Theater of Leptis Magna
- Temple of Zeus, Kirene
- Hatimin Hatimin Jami'ar Kasa, Libya
- Taswirar kasar
- Larabawan Libya
- Masallacin Karamanli, da ke tsohuwar Kasuwa, Tripoli Libiya
- Alzahra, Libya
- Wata Mata daga Libya
- Tutar kasar
- Birnin Tripoli Libya
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads