Eswatini

From Wikipedia, the free encyclopedia

Eswatini
Remove ads

Eswatini ko Swaziland bayan 2018 (da Swati: Umbuso we Swatini; da Turanci: Kingdom of eSwatini) ƙasa ce wacce babu wani teku da haɗu da wani yankin ta, da ke a Kudancin Afirka. Ta haɗa iyaka da Mozambik daga arewa maso gabas, da kuma Afirka ta Kudu daga arewa, yamma, kudu, da kudu maso gabas. Tana da ƙarancin faɗin ƙasa kimanin 200 km (120 mi) daga arewa zuwa kudu, da kuma kilomita 130 km (81 mi) daga gabas zuwa yamma, Eswatini tana ɗaya daga cikin mafi ƙananan ƙasa a Afurka, duk da haka, yanayin sararin samaniya na ƙasar ya bambanta, yana juyawa daga sanyi irin na tsaunuka zuwa zafi da rani irin na sauran yankunan kwari.

Quick facts Take, Kirari ...
Thumb
File:Mbabane, Eswatini
Thumb
Bankin Eswatini

Eswatini tana da yawan fili kimanin kilomita arabba'i 17,364. Eswatini tana da yawan jama'a kimanin 1,093,238, bisa ga jimillar 2017. Mafi yawancin jama'arta sun kunshi Kabilar Swazi. Babban birnin eSwatini shine Mbabane.

Sarkin (Ngwenyama) eSwatini Mswati III ne. Ndlovukati (uwar sarkin) Ntfombi ce. Firaministan ƙasar Cleopas Dlamini ne.

Thumb
Taswirar Eswatini
Thumb
Tutar eSwatini.
Remove ads

Hotuna


Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Remove ads
Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads